Wata yarinya 'yar shekara tara Aisha AbdulAleem, ta maka Gwamnatin jihar Ogun tare da shugaban karamar Makarantar Sakandarae ta Gateway Mrs Kushimo a gaban wata babban Kotu jiha da ke Isalo a Abeokuta, bisa zargin cin zarafinta ta hanyar hanata saka Hijabi a Makarantar
Aisha ta hannun Mahaifinta Mr. Muhammad AbdulAleem, ta gurfanar da shugabar Makarantar ne a Kotu saboda ta cire wa Aisha Hijabi da karfin tsiya, kuma ta hanata shiga aji domin ta dauki darasin karatu..
Cikin wadanda ake kara har da Kwamishinan Ilimi na jihar Ogun, Atoni janar kuma Kwamishinan shari'a na jihar Ogun, da kuma Gwamnatin jihar Ogun.
Lauyan Aisha, Olusoji Odutan, ya ce an shigar da karar ne domin neman Kotu ta haramta mataki da Makarantar ta dauka na hana Aisha shiga Makarantar da Hijabi. Ya ce yana kuma bukatar Kotu ta ayyana cewa wannan mataki haramtacce ne.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi