Type Here to Get Search Results !

Yanzu-yanzu: Wani Gwamna ya mutu a hadarin jirgi mai saukar angulu

Wani jirgi mai saukar angulu ya fadi sakamakon hadari da ya yi bayan ya bugi wani dogon karfe na sadarwa yayin da yake shawagin neman ya sauka. Lamari da ya sa jirgin ya kama da wuta a sararin samaniya kafin ya fado kasa tare da jama'ar da ke cikinsa a jihar Al-Qadarif na kasar Sudan.
Daga cikin wadanda suka mutu a wannan hadari har da Gwamnan jihar Al-Qadarif Mirghani Saleh, da wani babban jami'in gwamnatinsa, Kwamishinan yansanda na jihar tare da Ministan ayyukan gona.
Yawancin jiragen soji na kasr Sudan kirar jirage ne da aka yi odan su daga tsohuwar hadaddiyar daular Sorviet wadda ta wargaje a karni na 90's.
A watan Oktoba da ta gabata, wasu jiragen sojin kasar Sudan sun wargaje sakamakon hadari bayan sun yi karao da juna a hanyar zura ka sheka na jiragen sama a filin saukar jiragen sama na Khartoum.
Haka zalika, a watan Satumba da ta gabata, wasu matuka jirgin sama na sojin sama na kasar Sudan sun mutu bayan jirgin su ya fado daga sararin samaniya a birnin Omdurman wacce ke kusa da babban birnin kasar Sudan wata Khartoum.
DAGA ISYAKU.COM 
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG 
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebb

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN