Type Here to Get Search Results !

Main event

Yanzu yanzu: Dalili da ya sa muka kai samame a gidan yayan Atiku - EFCC

Sakamakon jita-jita cewa hukumar EFCC ta kama yayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar, hukumar ta fitar da wata sanarwa da Mujallar Labaran isyaku.com ta samu.
Hukumar ta ce "kamun da aka yi wa Ogbonna Orji, dan Theordore Orji kan zargin badakalar kudi baya da alaka da dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Tsohon Gwamnan jihar Abia na fuskantar bincike a hannun hukumar kan badakalar kudi, kuma hukumar tana zargin an gudanar da wannan harkalla ce da hannun yayan shi.

Kuma hukumar EFCC ta sa ido kan wasu motoci da yayanshi suka saye, a ranar Juma'a da ta gabata, jami'an hukumar sun gano motocin a wani gidan rawa watau Club a birnin Abuja, kuma jami'an hukumar suka yi hakuri suka jira domin su kama masu motocin.

Da misalin karfe 5 na Asuba jami'an hukumar suka kama Ogbonna da abokinsa Kelvin Ilonah, kuma suka jagoranci jami'an zuwa gidan da suke zaune da aka gano cewa an karbi hayanshi ne akan Naira miliyan 13 a kowane shekara.

Wadannan matsa sun ba hukumar muhimman bayanai wanda ke taimakawa abincike da hukumar ke yi.

Sakamakon haka muke son a gane cewa, hukumar bata je domin ta kama yayan Atiku ba, kuma EFCC bata kama yayan Atiku ba".
DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies