• Labaran yau

  'Yansandan jihar Kebbi sun yi babban kamu, da nassara kan 'yan fashi da makami | isyaku.com

  Isyaku Garba Birnin kebbi 21-12-2018

  Kwamishinan 'yansandan jihar Kebbi CP Kabiru Ibrahi, ga gargadi 'yan daban siyasa cewa duk wanda aka kama da makami a wajen kampen na siyasa zai gamu da fushin hukuma domin rundunarsa za ta gurfanar da shi a gaban Kotu. Hakazalika, ya gargadi marasa gaskiya a ko ina suke a cikin jihar Kebbi su tuba su daina aikata laifi ko su kwashe tarkacensu su bar jihar Kebbi domin rundunarsa ba za ta lamunci ayyukansu ba.

  Kwamishinan, ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar 'yansanda da ke jihar Kebbi ranar Juma'a.

  Hakazalika ya ce, rundunar 'yansanda na jihar Kebbi ta karbi koke koke kan aikata manyan laifuka kamar fyade, fashi da makami, da kisan kai guda 109. Ya kuma fayyace cewa rundunar ta kama mutum 872 bisa tuhumar aikata laifi, kuma ta gurfanar da mutum 872 a Kotu, an sami mutum 422 da laifi kuma suna Kurkuku, yayin da mutum 450 ke jiran shari'a.

  Yansndan sun kuma kama babura 26, bindigogi 9, bindiga kirar harba sheka 10, karamar bindigar hannu 4 da sauran tarin makamai.

  Kwamishina Kabiru, ya zagaya da manema labarai inda ya nuna su ga 'yan Jarida, ciki har da wadanda suka kwace mota a hannun wani Likita daga jihar Kaduna kwanaki 6 da suka gabat, kuma aka kamasu a jihar Kebbi, sai kuma wani da ke cikin 'yan fashi da suka shiga gidan wani Alhaji a kauyen Sandare shekarn jiya har aka kashe 'yan fashi biyu daga cikinsu.

  CP Kabiru, ya kuma nuna wa manema labarai wani wanda ya shahara wajen danfaran mutane ta hanyar amfani da wayar salula, hakazalika, ya gabatar da wasu 'yan fashi da makami da kuma wasu masu tsibbun yin kudi da farar zaiba, 'yan asalin kasar jamhuriyar Benin da dai sauran wadanda ake tuhuma da aikata laifi da dama.


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yansandan jihar Kebbi sun yi babban kamu, da nassara kan 'yan fashi da makami | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });