Rahotanni daga jihar Delta , sun ce ana zargin wasu 'yan banga sun kashe wani matashi har lahira. Wanda aka kshe mai suna Boss Destiny ya yi wata zafafar cacan baki ne tare da wasu mutane a wannan dare yayin da yake dawowa daga gidan rawa, watau Night Club a unguwar Sapele.
Wata majiya ta ce, wasu soji sun sasanta rigimar tsakanin Boss da daya bangaren. Amma yayin da ya shiga unguwarsu, sai wasu 'yan banga suka harbe shi da bindiga a kirji. Amma bayan ganin cewa Boss ya mutu, ana zargin cewa 'yan bangan sun je sun tone rami sai suka bizine sshi domin kada a gane.
Sai dai bayan wani abokin Boss ya labe kuma ya gan abin da aka yi ma Boss, sai ya je gida ya shaida ma 'yan uwan Boss wadanda suka je suka shaida wa 'yansanda, kuma 'yansanda suka shiga bincike da ya kai ga kama wadannan 'yan banga, kuma suka kai 'yansanda wajen da suka bizine Boss, daga bisani 'yansanda suka tone kabarin suka fito da gawar Boss domin gudanar da binciken kimiyya na Asibiti.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi