• Labaran yau

  Yadda matasa suka zartar ma wasu yan fashi hukuncin kisa ta hanyar duka suka konesu

  Wasu mutane da ake zargin yan fashi da makami ne sun gamu da ajali sakamakon hukuncin kato da wasu fusatattun matasa suka zartar masu bayan an an yi zargin cewa sun yi kokarin kwace wani Keke Napep daga hannun matukinta a babban kasuwar Ariara da ke birnin Aba a jihar Abia ranar Alhamis.

  Matasa sun harzuka bayan ganin abin da ya faru kuma nan take jama'a suka fara jibgan wadannan yan fashi, da makamai da duwatsu hai sai da yan fashin suka yi mutuwar gaggawa na dole sakamakon dakan turmi da suka sha a hannun wadannan matasa, kuma daga bisani aka bankawa gawarsu wuta suka kone kurmus.

  A mako da ya gabata, Mujallar isyaku.com ya kawo maku labarin wasu matasa guda biyu da jama'a suka kashe a birnin Aba, wadanda suka shahara wajen kwace kudin jama'a idan sun fito daga Banki, wadannan matasan sun kwace jakar kudi ne a hannun wani mutum da ya fito daga wani Banki bayan ya zari kudi , sai barayin su biyu a kan babur suka bi shi suka karbe jakar kudin suka karama babur dinsu wuta ssuka tsere.

  Amma sai Allah ya tona asirinsu domin shi wannan mutum tare da sauran jama'a da ke wurin sun kuwata kuma sauran jama'a suka bi barayin da suke kan babur dinsu bayan sun cafke jakar kudin, garin gudu ne sai daya daga cikin barayin ya fado daga wannan babur saboda tsananin gudu da baudiya a titi, sakamakon haka sauran jama'a suka same shi a kwance a kan titi kuma suka zartar masa da hukuncin Kotun kato na kisa ta hanyar duka. Kuma daga bisani suka kone gawarsa kurmus.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda matasa suka zartar ma wasu yan fashi hukuncin kisa ta hanyar duka suka konesu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });