• Labaran yau

  Wani mutum ya kashe 'ya'yansa 4, ya banka wa gidansa wuta, kuma ya rataye kansa

  Wani mutum da ba a gane ko waye ba kawo yanzu, ya kashe 'ya'yansa guda hudu, daga bisani ya banka ma gidansa wuta, sai ya rataye kansa har ya mutu a garin Alesa na karamar hukumar Elema, a jihar Rivers ranar Talata.

  Mujallara Labarai na isyaku.com ya gano cewa wannan mutum dan asalin garin Ogoja ne a jihar Cross Rivers. Yana zaune tare da matarsa a gida mai dakuna biyu tare da yaransa su hudu.

  Amma wata majiya ta shaida mana cewa, wannan mutum ya sami matsala tare da matarsa da dare da ya kai su ga rigima, sakamakon haka matar ta gudu ta bar gidansa. Bisa wannan dalili ne wannan mutum ya cika da fushi, kuma kai tsaye ya je ya dinga kashe yaransa, daya bayan daya, su hudu gaba daya.

  Daga bisani kuma ya banka ma gidansa wuta sai ya rataye kansa har ya mutu.

  'Yansanda sun je wajen da lamarin ya faru, kuma tuni suka dauke gawakin daga wannan wuri.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani mutum ya kashe 'ya'yansa 4, ya banka wa gidansa wuta, kuma ya rataye kansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });