• Labaran yau

  Tap di, mata da 'dan uwan matacce sun yi yajin hana a bizine gawa a raminta, ga dalili | ISYAKU.COM

  Mataki da 'dan uwa da matar wani mamaci dan shekara 33 suka dauka a kabarin mataccen ya ba jama'a masu makoki mamaki, bayan mutanen biyu sun shiga kabarin da za'a bizine mamacin suka yi kaka gida wai ba za su fita ba sai an yi adalci ga mamacin da aka kashe shi a gonarsa a mako da ya gabata.

  Wanan lamarin ya faru a garin Wanyororo da ke Bahati, a gundumar Nakuru a kasar Kenya.An sami gawar mamacin a gonarsa, bayan an daba masu wuka sau takwas a jikinsa ranar 3 ga watan Disamba.

  Majiyar Mujallar isyaku.com ta gano cewa, 'dan uwan mamacin da matarsa sun shige ramin kabarin ne domin 'yansanda da suka gudanar da bincike kan lamarin sun saki wanda ake zargin ya kashe dan uwansu mai suna Edward Mwangi, kuma a ranar da suka kamashi, bayan ya kai kanshi caji ofis na 'yansanda, tare da wukar da ya yi amfani da ita ya kashe Edward.

  Bisa wannan hujja ne, matar marigayi Edward da 'danuwanshi suka shiga yajin aikin kin barin a bizine gawar har sai an yi wa gawar adalci.

  Daga bisani dai an roke su, su fita daga ramin kabarin, bayan sun ki, mahaifin mamacin ya sa aka fitar da 'danuwan mamacin da matarsa daga ramin kabarin da karfin tsiya, daga bisani kuma aka bizine Edward da misalin karfe 2:00 na ranar Alhamis.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tap di, mata da 'dan uwan matacce sun yi yajin hana a bizine gawa a raminta, ga dalili | ISYAKU.COM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });