• Labaran yau

  Ta zarge ni da kallon duwawun Karuwa kuma tana wulakanta ni, miji da ya kashe matarsa

  isyaku.com 03-12-2018
  Yansandan jihar Ogun sun kama wani Barunje ko Mahauci mai suna Shina Kasali dan shekara 38 bayan ya yi sanadin ajalin mai dakinsa mai suna Sofiat, sakamakon tsananin duka da ya yi mata ranar Asabar a unguwar Abosule da ke garin Agbado na karamar hukumar Ifo.

  The Nation ta ruwaito cewa rigimar ta samo asali ne bayan mai dakinsa ta yi zargin cewa mijinta yana kallon duwawun wata Karuwa da ke daya gefen daga gidansu. Lamari da ya harzuka mijinta Shina, kuma sai mai dakinsa ta ce za ta je ta debo ruwa, shi kuma ya hana ta domin kada ta je ta tunkari Karuwar da rigima.

  Wannan lamari ne ya zafafa yanayin, daga bisani kuma sai dambe ya kaure inda Shina ya lakada wa matarsa Sofiat dan karen duka har ta suma, kuma yayin da ake kokarin kai ta Asibiti sai rai ya yi halinsa a hanya.

  Bayan yansanda sun kama Shina dangane da mutuwar matarsa, ya shaida wa yansanda cewa shi Mahauci ne wanda ke sana'ar Fawa da sayar da Nama, amma yan watannin baya harkoki sun tsaya kuma ya rasa aikin yi, sakamakon haka mai dakinsa ta yi amfani da wannan dama tana wulakanta shi kuma tana raina shi, har ma da ci masa zarafi domin kuncin rayuwa na rashin aikin yi da ya sami kanshi a ciki.

  Yan sanda dai na ci gaba da bincike a kan wannan lamarin, kuma tuni aka kai Shina hedikwatar yansanda sashen manyan laifuka a babban birnin jihar Ogun.
  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ta zarge ni da kallon duwawun Karuwa kuma tana wulakanta ni, miji da ya kashe matarsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });