Siyasa Ba Da Gaba Ba, Kalli Postan APC A Gefen Ofishin PDP A Birnin Kebbi | isyaku.com

Masana harkokin siyasa sun ce babban nassara da kowane 'dan siyasa zai iya samu shi ne sa'a da aka yi ta hanyar gudanar da siyasa ba da gaba ba. A unguwar Haliru Abdu kan titin da ke biyewa ta Magamar titunan kusa da tsohon ofishin CID a Birnin kebb, an kula da yadda aka baje posta na siyasa dauke da hoton shugaba Buhar tare da Gwamna Atiku Bagudu a APC, a gefe 'daya kuma, sai ga ofishin yakin neman zabe na Abu Geda, wanda shi ne 'dan takarar kujerar Sanata a Kebbi ta tsakiya a karkashin jam'iyar PDP.

Wani ma'abuci zama a Majalisi da ke gefen wannan ofis na PDP inda kuma aka baje posta na APC a kusa da shi, ya shaida wa Mujallar isyaku.com cewa, " Babu wata damuwa a kan baje wannan posta na APC a kusa da ofishin yakin neman zabe na Abu Geda. Muna zaune lafiya tare da cu'dani na fahimtar juna, sukan zo Majalisarmu mu ma mukan hau sama mu same su a ofishinsu domin mu sada zumunta, kuma tare da fahimtar juna.Babu wata matsala a kan wannan".

A ranar Laraba 26 ga watan Disamba 2018 ne jam'iyar APC na a jihar Kebbi ta kaddamar da yakin neman zabe na jiha a garin Argungu, a wani kasaitaccen taro da ya sami halartar dubban magoya bayan jam'iyar a fadin jihar


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post