Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kori wasu jami'anta guda uku daga aiki, bayan wata Kotun musamman na sojin ruwa ta samesu da laifin aikata sata a cikin watan Yuni na bana, a Mieka Jetty da ke garin Warri, inda sojin ruwan su uku suke aikin tsaro (Duty) .
Wadanda aka kora sun hada da Petty Officer Ekong
Samuel, Leading Seaman Elijah Sagwada da Seaman Usman Shuaibu, korar za ta fara aiki daga ranar 20 ga watan Disamba 2018, daga bisani kuma za a mika su ga hukumar gidajen Kurkuku na Najeriya da ke garin Okere Warri domin su yi zaman Kurkuku na wata biyar kowannnensu, bisa hukuncin Kotun sojin ruwa da ta same su da laifin aikata sata.
Sanarwar haka ta fito daga bakin babban kwamandan sojin ruwa Commodore Ibrahim Dewu, yayin da yake yi wa manema labarai bayani a jirgin ruwan soji NNS Delta da ke sansanin mayakan ruwa a Warri ranar Laraba.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi