• Labaran yau

  Makiyayi ya make 'dansa da sanda har ya mutu bisa zargin yana neman matarsa

  Rundunar 'yansandan jihar Niger ta gurfanar da wani makiyayi 'dan shekara 30 mai suna Kabiru Hassan, a gaban wata Kotun Majistare a birnin Minna na jihar Niger bisa tuhumar kisan kai.
   
  Mai gabatar da kara na 'yansanda,  ASP Daniel Ikwoche, ya shaida wa Kotu cewa Kabiru ya kashe 'dansa da ya haifa ne ta hanyar make shi da sanda a wuya, bisa zargin cewa 'danshi na neman matarsa, sakamakon haka kuma 'danshi ya mutu a dalilin wannan duka da sanda a wuyarsa ranar 7 ga watan Disamba da misalin karfe 11:00 na dare, a kauyen Tsako da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Niger.

  Alkalin Kotu ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 30 ga watan Janairu 2019, kuma ya bayar da umurni a tasa keyar Kabiru zuwa Kurkuku har zuwa zaman Kotun na gaba.

  Hakazalika ya umurci 'yansanda su yi kopi na takardun shigar da kara, kuma su kai ofishin DPP domin samun shawara bisa shari;ar da ake yi.
   
  DAGA ISYAKU.COM 
   
  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
   
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG 
   
  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Makiyayi ya make 'dansa da sanda har ya mutu bisa zargin yana neman matarsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });