• Labaran yau

  Ko a Musulunci ya dace miji ya tsotsi al'aurar matarsa har ta yi inzali ? Karanta amsa

  Isyaku Garba 02-12-2018

  Tambaya a yau ta fito daga Kabiru Sani Rano, Kano. Ko ya dace miji ya dinga tsosar Al'aurar matarsa har ta yi inzali?.

  Amsa  daga Malam Abbas Bello Birnin kebbi: Assalamu alaikum, wannan tambaya na da kyau saboda dukkannin Annabawa sun yi aure saboda haka wannan abu na matsalar iyali miji ya tsotsi al'aurar matarsa har ta yi inzali, in za mu tuna a cikin Alqur'ani a cikin Suratul Baqara sura ta biyu aya ta 223 "Allah ya ce matan ku gonakinku ne ku je ma gonakinku duk yadda kuke so amma a duk lokacin da za ku sadu da su, ku sadu da su ta gabansu ba ta bayansu ba, ma'ana kada a sadu da su a Duburar su. Amma duk yadda za ka yi, ta baya ne za ka saka Azzakarinka zuwa ga al'aurar matarka, ko ta ina ne, amma dai a sadu da ita a gabanta watau a al'aurarta".

  "Allah ya ci gaba da cewa ku ji tsoron Allah, ku sani za ku hadu da Allah, ku yi bushara da masu imani". To wannan aya Malaman tafsiri da dama tun daga Sahabbanmu da Malaman Tafsiri, shugabansu shine Ibn Abbas. Domin Annabi Muhammadu SAW. shi ne shugaban kowa, amma idan muka ce a cikin Sahabbai shine Ibn Abbas, yana da dalibai irin su Saidu Ibn Jubair,zuwa su Mujaheed da sauransu, sun yi bayanai masu gamsarwa dangane da wannan, haka kuma an sami wasu Malamai irin su Ibn Khatir,irin su Kurfabi,irin su Jalalain duk sun yi bayanai game da wannan aya wanda ta kunshi abubuwa masu yawa.

  Wannan aya ta nuna mana Matan mu gonakin mu ne da za ka iya shiga , kuma gona za ka iya shiga ko ta ina, ta gabas,yamma,kudu ko arewa. A nan Musulunci ya yarda a yi hakanan matukar duk wani abin da za a yi domin ka faranta wa matarka rai, wannan shari'a ta baka dama ka yi shi. Amma akwai shaaruddan da Malamai suka gindaya.
  Malam Abbas Bello B-kebbi

  1. Sharadi na farko shine ya zama bata Haila, saboda idan ka tsotsi al'aurar matarka lokacin da jinin haila ke zuba ba mamaki ka kamu da wani cutu, ma'ana za ka iya hade jinin domin bai yiwuwa mutum ya tsotsi al'aurar matarsa a ce bai hadiye wani abu daga cikin lamurranta ba.

  2. Ya zama bata jinin biki, za ka iya tsotsar al'aurarta har ta yi inzali, wannan babu laifi.

  3. Wajibi ne matarka ta aminta da hakan kafin ka tsotsi al'aurarta, domin kila akwai mata da idan aka yi mata haka, za ta iya shiga wani rashin lafiya kilan sai ta yi sati daya a kwace domin bata saba ba da wannan. Idan dai kai ka aminta kuma matarka ta aminta, to wannan ba laifi a kan shi. Sannan kuma wannan abin idan mutum na yinshi, to za ka gan kuma wannan ya kara dankon zumunci tsakaninshi da matarsa.

  Daga karshe shari'ar Musulunci bata hana ba, ta bada dama mutum ya yi wannan matukar matarsa bata cikin wadancan sharudda guda uku da muka ambata..

  Sai dai Malamai sun ce kada wannan ya zama shi kadai ake yi, domin manufar aure shi ne a haihu, idan kuma ba a sa maniyi a cikin al'aurarta babu haihuwa kenan. Idan dai shi ne kadai ake yi mata misali suna zaune shekara 2 ko 4 kullum shi ne ake yi, to wannan akwaai matsala

  Amma idan dai wata rana ayi wannan wata rana kuma a yi saduwa na jima'i da za a sa maniyi a al'aurarta to wannan ba damuwa Insha Allahu.

  Mawallafi Isyaku Garba ya gabatar

  Malam Abbas Bello Birnin kebbi ya amsa tambaya

  Alh. Umar Namashaya Diggi, shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a jihar Kebbi ya dauki nayin shirin. Allah ya saka masa da mafificin alhairinsa tare da masu gabatarwa da sauran al'umma Musulmi.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko a Musulunci ya dace miji ya tsotsi al'aurar matarsa har ta yi inzali ? Karanta amsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });