Jam'iyar APC a jihar Kebbi ta karyata alakanta Gwamnatin jihar da sace wani dan siyasa | ISYAKU.COM


Jam'iyar APC na jihar Kebbi karkashin shugabanta Arc. Bala Sani Kangiwa, ta karyata jita-jita da ke yawatawa a kafofin sada zumunta wanda ke kazafin cewa yan jam'iyar APC 6000 sun koma jam'iyar PDP a fadin jihar daga yankin karamar hukumar Danko Wasagu da ke kudancin jihar Kebbi.

Hakazalika, jam'iyar APC ta musanta zargin cewa an sace wani dan siyasa daga wannan yankin Alh. Dan Musa Ribah, wanda ake zargin cewa gwamnatin jihar Kebbi ce ta sa aka sace shi tare da 'dansa. Bisa wannan dalili ne jam'iyar APC na jihar Kebbi ta yi Allah wadai da wannan labari, kuma ta zargi masu tsare-tsare na jam'iyar PDP a jihar Kebbi da kitsa wannan labarin kanzon kurege wanda ta ce kalamai ne da zargi da ake kirkiro domin a haddasa kiyayya da fitina a cikin al'umma.

Jam'iyar APC a jihar Kebbi har ila yau, ta kalubalanci jam'iyar adawa ta PDP a jihar, cewa ta karanto sunayen 'yan jam'iyar APC da suka caanja sheka zuwa PDP domin an ce inda babu kasa ne ake gardamar kokuwa.

Tuni dai aka gan Alh.Dan Musa Riba ya bayyana ranar 9/12/2018 a wani faifen bidiyo da aka dauka da wayar salula a gida, yana bayani cewa babu wanda ya sace shi kuma wannan labari ba gaskiya bane. Dan Musa ya yi ingantaccen bayani da ya wadatar da gaskiyar cewa labarin da ke zagayawa a yanar gizo dangane da lamarin ba gaskiya bane.

Wata majiya ta shaida wa Mujallar isyaku.com cewa, wani dan Jarida da ya wallafa wannan labari na sace Alh. Dan Musa Riba, tuni ya fuskanci fushin jami'an tsaro bayan ya kasa bayar da gamsashshen bayani kan inda ya samo wannan labari da ya wallafa.

Majiyar mu ta tabbatar mana cewa tuni jami'an tsaro suka gurfanar da dan Jaridan a gaban wata Kotu a garin Birnin kebbi, kuma Kotu ta bayar da ajiyarsa a Kurkuku har zuwa zaman Kotu na gaba dangane da karar, sakamakon tuhumar bayar da labarin karya da kuma wasu jerin tuhume-tuhume.


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN