• Labaran yau

  Ina son in jima yaron ciwo ne domin uban ya wahala a Asibiti, Mata da ta kashe dan makwabcinta

  'Yansanda a caji ofis na Tolu da ke Apapa a birnin Lagos ranar Laraba, sun cafke wata mata mai suna Ms. Chineye Ndubuife yar asalin jihar Anambra, bayan ta tabbatar cewa ita ce ta kashe 'dan makwabcinta yaro 'dan shekara 2. Shi dai wannan yaro 'dan Mr Promise Samuelne 'dan asalin karamar hukumar Ikono a jihar Akwa Ibom ne.

  Mujallar isyaku.com ya gano cewa, Chineye ta kashe wannan yaro ne da gangan. Wannan mata ta aiki yara da ke cikin dakinta su 3 cewa su je su sayo mata Indomie, lokacin da za su tafi su sayo mata Indomie, sai ta ce shi wannan yaro dan makwabcinta mai suna Wisdom ya tsaya ya jira su kamar yadda majiyar mu ta shaida mana.

  Bayan yaran guda 2 sun fita, sai Chineye da zagaya da wannan yaro zuwa ban daki ta kwada kanshi da bango, daga bisani kuma ta dauko dutse ta dinga kwada masa a kai hair wannan 'dan yaro mai suna Wisdom ya mutu, kana ta jefar da gawarsa a cikin masai ko ban daki.

  Amma da 'yansanda suka binciketa a kan musabbabin da ya sa ta kashe wannan 'dan karamin yaro, sai ta ce, " ban yi niyyar kashe shi ba, na so ne in raunata yaron domin mahaifinsa ya sha wahala kuma ya kashe kudi da yawa wajen jinyarsa, amma bana da niyyar kashe shi".

  Yanzu dai Mrs. Chineye tana hannun 'yansanda kuma tana amsa tambayoyi, yayin da suke ci gaba da bincike.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ina son in jima yaron ciwo ne domin uban ya wahala a Asibiti, Mata da ta kashe dan makwabcinta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });