• Labaran yau

  Gobara Ta Kone Gawaki 50 Da Aka Ajiye A Dakin Adana Gawa A Wani Asibiti

  Wata mumunar gobara da ta tashi a dakin ajiye gawaki na Asibitin Enugwu Ukwu a karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra ya yi sanaadin konewar gawaki 50 da aka ajiye a dakin adana gawa ranar Asabar 29 ga watan Disamba.

  Hukumar Asibitin bata ce komai ba lokacin da majiyarmu ta bukaci bayani kan lamarin kawo yanzu, domin mahukuntan Asibitin na cike da juyayin wannan lamari kafin lokacin da muka rubuta wannan labari.

  Majiyarmu ta ce ba mamaki yawan gawaki da suka kone zai iyasamun nasaba da dokar hana bizine gawa a watan Disamba da ake aiki da shi a jihar Anambra, wanda ya haifar da yawan gawaki da ba a bizine ba har guda 50, kuma suka kone kurmus a wannan gobara.

  'Yan uwa da abokan gawakin da suka kone, sun fashe da koke koke, wasu na faduwa a kasa, yayin da wasu ke birgima a kasa sakamakon bakin ciki da tausayi kan kamarin da ya faru da gawakin 'yan uwansu.


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gobara Ta Kone Gawaki 50 Da Aka Ajiye A Dakin Adana Gawa A Wani Asibiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });