• Labaran yau


  Duba adadin sojin Najeriya da suka mutu a Buni Gari

  RFI Hausa

  Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojin ta guda 8 lokacin da mayakan boko Haram suka kai musu hari a sansanin su dake Buni Gari a Jihar Yobe.
  Kamfani dillancin labaran Faransa ya ce daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka ya tabbatar masa da aukuwar lamarin.

  A karshen makon da ya gabata ne mayakan book Haram suka kai harin, wanda ke zuwa kwanaki bayan na Matelel.

  A lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri ya sha alwashin yin amfani da duk wata dama da tsarin mulkin Najeriya ya tanadar masa wajen samar da kayan yaki na zamani don kawo karshe abinda ya bayyana da haukar da mayakan Boko haram ke yi.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba adadin sojin Najeriya da suka mutu a Buni Gari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama