Wata 'yar Majalisar wakilai kuma mai magana da yawun masu tafiyar da kwamitin yakin neman zabe na shuagan kasa a jam'iyar PDP Nnena Ukeje ta ce dalilin da ya sa 'yan Majalisa suka yi ma shugaba Buhari ihu a zauren Majalisa yayin da ya gabatar wa Majalisa da kasafin kudi na 2019 shi ne " Marmakin Buhari ya fuskanci abin da ya kawo shi zauren Majalisa, sai ya mayar da lamarin tamkar yakin neman zabe na jam'iyar APC a matsayinshi na wanda ke rike da tutar 'dan takarar jam'iyar APC".
Ta yi wannan jawabi ne yayin da ta bayyana a gidan Talabijin na Channels ranar Litinin. Ta kara da cewa " abin da shugaba Buhari ya kamata ya yi shi ne, "Da ya koyi halin tsohon shugaba Jonathan, wanda ya gabatar da kasafin kudi kafin zaben a yanayi na saukin kai da fahimta".
" A wannan yanayi da lamura suka yi zafi, shugaba Buhari har ma ya daga hannayensa guda biyu daidai yadda APC ke nuna zarcewa a yanayin yakin neman zabensu. Irin wannan hali dole ne ya zafafa lamurra a wannan lokaci domin dai akwai 'yan jam'iyar PDP masu yawa a wannan zaure da 'yan jam'iyar APC suka dau shewa daidai lokacin da shugaba Buhari ya yi wadannan ababen".
"A matsayinka na 'dan Najeriya, kamata yaa yi ka auna ka gani, shin rayuwarka ta inganta tun 2015 zuwa yanzu ko a'a ? wannan shi ne ya kama kowane 'dan Najeriya ya duba".
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi