Ba 'Dansanda Da Ya Tsere Daga Bakin Aikinsa A Wajen Fada Da Boko Haram - Kakakin 'Yansanda

Hedikwatar hukumar 'yansandan Najeriya ta karyata rahotun da ke cewa jami'anta 167 cikin 2000 da aka ba horon musamman domin su yi fada da 'yan Boko Haram a jihar Yobe sun tsere.

Wani rahotu ya ce jami'an na 'yansanda sun tsere daga bakin aikinsu har ma an sako sunayen wasu jami'an 'yansanda da aka ce suna daga cikin wa'danda suka tsere kuma aka wallafa sunayen a shafukan intanet.

Amma Kakakin hukumar 'yansandan Najeriya Jimoh Moshood, ya karyata labarin a wata sanarwa da ya fitar a shafin hukumar 'yansanda na kafar sada zumunta.

Moshood ya ce, musamman 'yansandan kwantar da tarzoma Mopol, suna kan gaba tare da sojin Najeriya a fagen daga wajen fada da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post