• Labaran yau

  Azabar yawan jima'i da matarsa ya sa yansanda sun umurci magidanci ya bar gidansa

  Yansanda a sashen rundunar yansanda na Ikotun a birnin Lagos sun ba wani mutum mai suna Solomon Udochukwu wanda ke unguwar Prophet Amowo , a bus stop na Onitire umurnin ya bar gidansa bayan ya sha maganin kara karfin mazakuta kuma ya ke wahalar da matarsa Ijeoma lamari da matar ta ce ya shafi yayansu kanana guda biyu.

  Majiyar Mujallar isyaku.com ta gano cewa yansanda sun dauki wannan matakin wucin gadi ne domin su maido da zaman lafiya a gidan kasancewa lamarin yakan shafi yaran ma'auratan.

  Rahotanni sun ce Solomon ya kori matarsa da yayanta biyu daga gidansa bayan ta ki ta yi jima'i da shi saboda ta gano yana shan maganin sa namiji ya dade a kan mace lokacin jima'i kafin ya yi inzali, lamari da Ijeoma ta ce hakan ya sa ta kusa mutuwa a jima'i da suka yi da Solomon kafin yanzu.

  Sakamakon haka Ijeoma ta kai kara wajen yansanda wadanda suka zo suka bude kofar gidan da karfi, kuma Ijeoma da yayanta suka shiga.

  Daga bisani Solomon ya tunkari yansanda amma sai suka shaida masa cewa sai dai ya yi hakuri ya nemi wani muhalli amma kada ya sake ya shiga gidansa, saboda abin da ya aikata ya jefa matarsa da yayansa cikin tsoro da matsanancin fargaba.

  Majiyarmu ta ce yanzu haka Solomon ya bi umurnin yansanda ya kaurace ma gidansa.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Azabar yawan jima'i da matarsa ya sa yansanda sun umurci magidanci ya bar gidansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });