• Labaran yau

  An tallafa wa matan 'yansanda Mopol 11 daga jihar Kebbi da suka mutu a Zamfara

  Isyaku Garba - Birnin kebbi - 23-12-2018


  Uwargidan Kwaminshinan 'yansandan jihar Kebbi Hajiya Binta M. Kabir, amadadin Uwargidan Safeto janar na 'yansandan Najeriya Hajia Hasfsat Ibrahim K Idris, ta gabatar da tallafi domin jajenta wa matan 'yansandan kwantar da tarzoma guda 11 da suka rasa rayukansu a fagen daga da 'yan ta'adda a jihar Zamfara makonnin da suka gabata.

  'Yansandan kwantar da tarzoma guda 11 daga MOPOL 36 na jihar Kebbi, sun gamu da ajalinsu yayin da suke gudanar da aikin tsaro a jihar Zamfara. Wannan shi ne ibtila'i na farko da ya shafi jami'an 'yansandan kwantar da tarzoma na MOPOL 36 har guda 11 lakaci daya da aka tabbatar da nagarta, juriya da sadaukarwa wajen gudanar da aikin tsaro a Najeriya.

  Hajiya Binta, ta ce " babu wata kalma da za ta iya dawowa da wa'dannan jaruman 'yansanda da suka sadaukar da rayukansu, suka biya babban farashi na rasa rayukansu domin tabbatar da tsaro a yankin Zamfara da Najeriya baki daya".

  "Allah ya baku hakurin wannan babban rashi, kuma Allah ya yi maku mafita ya taimake ku tare da yaran da mazajen ku suka bari, kuma Allah ya albarkaci wadannan yara".

  Ta kuma mika kyautar N50.000, buhun shinkafa 1 tare da Jarkan Mai ga kowace mace da mijinta ya rasu, amadadin Uwargidan Safeto janar na 'yansandan Najeriya.

  A nashi jawabin, shugaban 'yansandan kwantar da tarzoma na Squadron 36 jihar Kebbi CSP Isyaku Usman,ya yi godiya ga Uwargidan Safeto janar na 'yansanda da Uwargidan Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi, bisa wannan kokari da suka yi na bayar da wadannan kayakin tallafi ga iyalan jami'an MOPOL su 11 da suka kwanta dama.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An tallafa wa matan 'yansanda Mopol 11 daga jihar Kebbi da suka mutu a Zamfara Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });