• Labaran yau

  An bizine gawakin yan fashi 2 da aka kashe a Sandare na karamar hukumar Kalgo jihar Kebbi | isyaku.com

  Isyaku Garba - Birnin kebbi - 19-12-2018

  Wasu mutum biyu, sun gamu da mumunar ajali a kauyen Sandare da ke kusa da garin Makera a karkashin karamar hukumar Kalgo da ke jihar Kebbi a daren ranar Talata, bayan sun aikata fashi da makami tare da gungun 'yan uwansu 'yan fashi a garin Sandare. Amma bayan sun gama aikata fashi, lokacin da suke kokarin ficewa daga garin, sai wani 'dan banga ya fake ya harbi mutum biyu daga cikinsu.

  Bayan 'dan banga ya harbi mutanen guda biyu, sai suka galabaita, har jama'ar gari suka iso suka karkare su da dukan ajali, kuma suka yi ma gawakin munanar raunukan sara da adduna da kulake, daga bisani aka barsu jina-jina cikin mumunan yanayi.

  Majiyar ISYAKU.COM ya ce "'Yan fashin su shiga garin Sandare ne da dare ranar Talata, kuma suka je gidan Alhaji Shehu Sandare, suka bukaci ya bude kofa, amma da ya ki, sai suka hau kan rufin gidansa, suka fara yanke kwano. 'Yan fashin, sun karbi Naira Miliyan 2.5 watau Miliyan biyu da dubu dari biyar daga gidan Alhaji Shehu".

  "Karar harbe harben bindigogi daga 'yan fashin ya game garin Sandare cikin wannan dare, yanayi da ya sa jama'an gari suka tashi cikin fargaba. Bayan 'yan fashin sun kammala karbar kudaden ,sai suka kama hanyar fita daga garin Sandare, amma wani 'dan Banga ya labe, sai ya harbi biyu daga cikin 'yan fashin, wanda ya yi sanadin kama su, kuma har fusatattun jama'ar gari suka karkare aika su barzahu, yayin da sauran suka ranta da gudun fitar rai, kuma wasu jama'an gari suka bi su da gudu ko da Allah zai sa su kama su".

  Shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a jihar Kebbi, Alhaji Umar Namashaya Diggi, tare da tawagarsa har da jami'an tsaro na karamar hukumar Kalgo, sun yi isar gaggawa a kauyen, kuma suka tafiyar da tsare-tsare da suka kamata.

  Wata majiya ta shaida mana cewa, an tsinci wayar salula guda biyu na 'yan fashin wanda suka yar garin gudu, kuma an mika su ga jami'an tsaro domin gudanar da bincike. Hakazalika bayanai sun tabbatar cewa, tuni jami'an tsaro sun bi sawun wadannan 'yan fashi.

  Bayan jami'an tsaro sun kai gawakin mutum biyu da aka kashe zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin kebbi. ISYAKU.COM ya lura cewa gawakin sun gamu da wulakanci da yake da nassaba da mumunan karshe da suka yi, domin dai bayan wasu bayin Allah sun sayi ababen da suka wajaba domin yi ma gawakin sutura, an lura babu wanda ya yi ma wadannan gawakin wata addu'ar neman rahama daga Allah.

  Duk da yake an ga charbi a aljuhun wadannan 'yan fashi da aka kashe, amma an sami gureaye da layu a jikinsu, har da wasu guraye bakin saka da aka ce na Baduhu ne da kau da ido. Ala tilas wakilin mu ya kira ofishin Hizbah na jihar Kebbi domin su taimaka a yi ma wadannan 'yan fashi Sallar Jana'iza, domin hatta 'yan agaji da wakilinmu  ya tuntuba basu zo wajen Sallar Jana'izan ba.

  An yi ma barayin Sallar Jana'iza bayan Sallar Azaahar, da misalin karfe uku na rana , kuma aka kaisu Makabartar Dukku aka bizine su a Makabartar Musulmi da misalin karfe uku da rabi na ranar Laraba 19 ga watan Disamba 2018.Har aka bizine wadannan barayin ba wanda ya ce ya san su ko ya san inda suka fito.

  Daga cikin jami'an Hizbah na jihar Kebbi da suka Sallaci gawakin , kuma suka yi dawainaiyar kaisu Makabarta kuma suka bizine su, har da Alhaji Ibrahim Gwadangaji, Sakataren kwamitin Hizbah na jihar Kebbi, Mataimaikin shugaban Hizbah na jihar Kebbi Alhaji Mamuda Geza, sai Alh. Abubakar Udu, Mai ladabtarwa na Hizbah, Ali Baba Kardi, Mataimakin Sakatare na Hizbah, sai wakilan 'yansanda da suka hada da Safeto Yusuf Abubakar da Safeto Umar 'Dan Abba, sai kuma Alasan Abdullahi Hizbah, Direban motar Hizbah na jihar Kebbi tare da Ibrahim Yauri, Welfare na Asibitin Sir Yahaya da Mawallafin shafin ISYAKU.COM Isyaku Garba.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An bizine gawakin yan fashi 2 da aka kashe a Sandare na karamar hukumar Kalgo jihar Kebbi | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });