• Labaran yau

  Almundahana: Alkali ta suma a Kotu bayan EFCC ta gurfanar da ita a gaban wata Kotu | ISYAKU.COM

  An kasa ci gaba da shari'ar da ake yi ma wata Alkali Justice Rita Ofili-Ajumogobia bayan ta yanke jiki ta fadi ta suma, yayin da aka gabatar da ita a gaban Alkali a babban Kotun jihar Lagos ranar Juma'a kafin a fara shari'a.

  Wannan lamari ya sa Alkalin Kotun ya dage shari'ar har zuwa ranar 26 ga watan Janairu 2019. Bayan Alkalin ta suma , wasu Lauyoyi, iyali, 'yan uwa da abokan arzikin wannan Alkali sun yi harama zuwa wajenta domin su bayar da agajin gaggawa.

  Justice Rita Ofili-Ajumogobia tana fuskantar shari'a ne bayan hukumar EFCC ta gurfanar da ita bisa tuhumar almundahana, yin arziki ta haramtacciyar hanya, karbar cin hancin Naira miliyan biyar da sauran jerin laifuka har guda 26. Justice Rita tana fuskantar tuhuma ne tare da wani babban Lauya Ofili-Ajumogobia mai darajar SAN. Dukannin wadanda ake karar basu amsa laifin da ake tuhumarsu ba.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Almundahana: Alkali ta suma a Kotu bayan EFCC ta gurfanar da ita a gaban wata Kotu | ISYAKU.COM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });