Zargin dakatar da mataimakin shugaban APC na kasa ya haifar da rudani


Legit hausa

Rahotanni sun kawo cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen jihar Sokoyo ta dakatar da mataimain shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, kan zargin yin ayyukan da suka sabama jam’iyyar. Korar ta sa ta biyo bayan wani rubutaccen korafi da daya daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da ke mazaba daya da Inuwa, ta Magajin Gari Ward A, mai suna Na’ibi Abubakar ya rubuta kuma ya aika wa uwar jam’iyyar ta jihar Sokoto.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dakatar da Abdulkadir ya biyo bayan korafi da dan jam’iyyar APC da ke mazaba daya da Inuwa, ta Magajin Gari Ward A, mai suna Na’ibi Abubakar ya rubuta kuma ya aika wa uwar jam’iyyar ta jihar.

An zargi Inuwa mai lambar rajista da APC ta SOK/SON/04006510 da aikata laifukan da aka ce duk yi wa jam’iyya zagon-kasa ne, tozarta ta da kuma rashin maida hankali kan kulawa da hidimta wa jam’iyya. An tattaro cewa har yanzu Inuwa ya na nuna kusancin sa da Tambuwal da kuma sinsinar PDP da ya ke yi, domin har yau bai ajiye mukamin sa na Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Sokoto ba, mukamin da Tambuwal ya nada shi, a lokacin da gwamnan ke cikin jam’iyyar APC.

An kafa kwamitin da ya binciki wadannan zarge-zarge da aka yi wa Inuwa, kuma kwamiti duk ya tabbatar da gaskiyar haka. Wannan ce ta sa gaba dayan Mambobin Kwamitin Gudanarwar APC na jihar Sokoto su arba’in su ka sa hannun amincewa a kore shi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN