Yunkurin sace shi ne ko barazana, Babangida Danburam ya sha da kyar cikin daji

Wani labari da muka samu ya nuna cewa wasu mutane sun gayyaci Babangida Garba Gwandu daga gidansa da misalin karfe 8:45 na safe, kuma suka bukaci cewa Oga yana nemansa dangane da zancensu da ke wajen hukuma, daga nan suka fita tare da shi a kan babura.

Babangida ya kwaci kanshi da kyar bayan ya tsere daga hannun wadanda suka gayyace shi, kamar yadda ya shaida wa tsofaffin ma'aikatan gwamnati a Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a garin Birnin kebbi, bayan ya kula cewa mutanen sun nufi cikin daji da shi ta unguwar Kampanin Labana. Daga karshe ya tsere kuma ya fada cikin gonakin Albasa.

Bincikenmu ya nuna cewa yansanda basu sane da wannan lamari.

Sakamakon haka zamu kawo maku cikakken labarin abin da ya faru da zarar mun kammala tattara bayanai.

Babangida Garba Gwandu shi ne shugaban Pressure Group na tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi wanda aka kama sakamakon kara da gwamnati ta shigar wajen yansanda a kansa mako da ya gabata, bisa zargin aikata ba daidai ba da wasu kudade lokacin da yake shugabantar hukumar KUDA.


DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
 • 0/Post a Comment/Comments

  Rubuta ra ayin ka

  Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari