• Labaran yau

  Ya kama dan aiki da yar aikin gidansa suna lalata a cikin motarsa, wane hukunci ya dace da su?

  Sashen jakar magori na Mujallar Isyaku.com ya samo wani labari daga kudancin Najeriya saboda wani mutum mai suna  John Ikedi Mmaduegbunam ya shiga rudani kuma yana neman shawara daga jama'a, bayan ya kama Yaron gidansa mai yi masa aikin tsaron shago tare da yar aikin gidansa mai wanke wanke da share share suna lalata a cikin motarsa da dare.

  John Ikedi Mmaduegbunam ya ce " Na tashi da misalin karfe 2 na dare domin in yi fitsari, sai na kula cewa batur na wayata ya yi kasa matuka saura digo 4 kuma bamu da wutar lantarki a wannan unguwa cikin wannan dare.

  Bayan na je na yo fitsari na dawo, sai na je wajen mota ta domin in saka wayata a cajin cikin mota, amma bayan na je wajen motar, sai na gan Yaro na mai tsaron shago yana lalata da Yarinya mai aikin gidana. Ni fa na rude a kan wannan lamari.

  Tuni dai na tura yaron da yarinyar kauyukansu. Kuma shi wannan yaro ya shafe shekara 7 tare da ni yana yi mani aiki, kafin wannan lamari dama zan yaye shi ne a karshen watan 12 watau Disamba. Ina neman shawara kan irin hukunci da ya kamata in yi masa da ita yarinyar".

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ya kama dan aiki da yar aikin gidansa suna lalata a cikin motarsa, wane hukunci ya dace da su? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });