Legit hausa
Shahararriyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa, Fatima
Isa wacce aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa babu wani tasiri da
Fina-finan Indiyan Hausa zai yi kan na Kannywood duk da ko sun karade kasuwani.
Teema ta nuna farin ciki da cikar burinta wanda a cewarta
tuna tana yar kamarta burinta shine ganin kanta a masana’antar shirya
fina-finai, kuma gashi Allah ya cika mata wannan buri nata Jarumar ta bayyana
hakan ne a hira da tayi da Premium Times a jihar Kaduna.
Ta kuma bayyana cewa tun bayan fara bayyanarta a wasanni,
bata taba yin koda musayar yawu ba da wata ba ko wani Forodusa, ko Darekta.
Tace kowa takan dauke shi dan uwanta ne. Da aka tambaye ta ko rashin fitowar
fim a kasuwanni yanzu zai iya kawo wa masu shirya fim din wani matsala sai
tace: ”Babu wani matsala da hakan zai yi.
Sinima ake fara nunawa inda bayan an nuna a nan sai kuma a
sake shi a kasuwa. Ni banga wani matsala da yake kawo wa ba. ”A harka ta babu
matsala kuma ba zai shafi shanawar tauraro na ba.” Bayan nan Teema ta yabi wasu
daga cikin abokanan aikin ta kamar Fati Su, inda ta kurantata da cewa macece
mai kamar maza.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI