Legit hausa
A yau Alhamis ne shedu uku suka bayyana wa kotu yadda aka yi
Bilyaminu Bello da ake zargin matarsa, Maryam Sanda da kashe shi ya mutu.
Bello, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Haliru Bello ya rasu ne a
Nuwamban 2017.
An tuhumar matarsa
Maryam Sanda, mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; dan uwanta, Aliyu Sanda da mai aikin
gidansu, Sadiya Aminu da hannu cikin kisarsa. A yau Alhamisa ne lauya mai
shigar da kara, Fedelis Ogbebe ya gabatarwa kotu shedu uku, Hamza Abdullahi
(mai wanki da guga), Simon Okon da Usman Aliyu domin su bayyana kotu abinda
suka sani a kan rasuwar Bilyaminu. Ga abinda Mr Abdullahi mai wanki da guga a
gidan ya fadi:
"A ranar 17 ga watan Nuwamban 2017 misalin karfe 1-2 na
dare ina kwance sai na ji ihun Bilyaminu, na tashi na nufi idan ya ke sai na
samu ya rufe bangaren kirjinsa da riga, bayan mintuna biyu sai matarsa ta fito
rike da makulin mota ta bukaci mu taimake ta saka Bilyaminu cikin mota.
"Da mu kayi
kokarin daga shi sai muka ka jini. Ni da wasu mutane biyu muka saka shi cikin
mota yayin da matarsa ta tuka motar. Da muke cikin motar ta tambayi ni Asibiti
mafi kusa sai na fada mata Maitama Clinic. "Da isar mu asibitin mun hada
da nurse ta da kira mana likita. Likitan ya tambayi Maryam abinda ya faru har
sau uku amma ba ta amsa ba.
Hakan yasa likitan ya ce mu tafi dashi wani asibiti, daga
nan muka tafi Maitama General Hospital nan ma likita ya tambaya abinda ya faru.
"Daga nan ne Maryam ta fada wa likitan cewa suna ta fada ne da mijinta
tunda safe. Likitan ya duba Bilyaminu sai ya gano cewar ya mutu. Likitan ya
bukaci ta kira 'yan uwansu a waya amma ta ce masa wayanta da na mijinta sun
lalace wajen fada.
Ya bata wayansa ta kira yan uwanta ta fada musu abinda ya
faru. "Yan uwanta sun taho daga baya suka karbi gyalenta suka rufe gawar
Bilyaminu. Daga nan mahaifiyar Bilyaminu ta iso ta bude fuskan dan ta inda ta
lura akwai alamar yankan wuka a kirjinsa da cizo a kirjinsa da kunnensa. Akwai
yanka a yatsansa da kuma al'auransa.
"Da komawarmu
gida sai na lura cewa an goge jinin da muka bari kafin zuwa asibiti, na tambayi
Alabi ko shine ya goge jinin amma ya ce ba shi bane." Mr Okon ASP na yan
sanda shima ya bayar da nasa labarin abinda ya sani. Kazalika Mr Aliyu, abokin
Bilyaminu shima ya fadawa kotu abinda ya sani game da rasuwar. Bayan sauraron
dukkan shaidun, alkalin kotun mai shari'ah Yusuf Halilu ya dage cigaba da
sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba.
DAGA ISYAKU.COM
Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI