• Labaran yau

  Matashi ya taushe mahaifiyarsa ya yi lalata da ita, ya kuma yi lalata da surukarsa

  Isyaku Garba 4-11-2018
   
  Wani matashi dan shekara 32 mai suna Shekari David ya fada hannun yansanda a jihar Kaduna sakamakon yi wa mahaifiyarsa yar shekara 65 fyade, hakazalika Davi ya kuma yi ma surukarsa yar shekara 70 fyade, hakazalika fitacce ne wajen aikata laifukan fashi da makami a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

  Majiyarmu ta gano cewa David dan giya ne na gaske, kuma ya shahara wajen yi wa tsofaffin mata fyade a duk lokacin da ya bugu bayan ya kwankwadi barasa.

  David ya shaida wa yansanda cewa ya taba yi wa mahaifiyarsa fyade da tsakiyar dare bayan ya bugu da barasa, ya ce bayan ya isa gida ya tarar da ita tana barci, sai ya lallaba ya shigeta ya fara lalata da ita, ya ce jin haka ke da wuya sai mahaifiyarsa ta fasa ihu, jama'a suka zo , daga bisani ya sha dan karen duka a hannun makwabta.

  Ya kara da cewa bayan haka, da safe ya tafi ya gurfana ya nemi mahaifiyarsa gafara a kan abin kunya da ya aikata da ita, kuma ta aminta ta yafe mashi ganin cewa yana cikin barasa ne lokacin da ya aikata wannan aiki. Amma ya ce ganin haka ke da wuya sai matarsa ta yi fushi ta tafi gidansu, daga bisani ta kashe aure ta auri wani mutum.

  Ya kuma ci gaba da bayani cewa ya je kauyen matarsa watau Mahuta, domin halartar wani biki, amma sai ya kwankwadi barasa ya yi tatil, hankali ya gushe, sakamakon haka da tsakiyar dare sai ya nufi gidan surukarsa watau mahaifiyar matarsa, ya tarar ta riga ta yi barci da tsakiyar dare, sai ya lallaba ya shige ta ya fara lalata da ita, jin haka ke da wuya sai tsohuwar yar shekara 70 ta kwala kururuwa don neman ceto.

  Bayan makwabta sun shigo dakin ne sai suka tarar da gogan naka David ne ya yi ma surukarsa shige har ya aikata lalata da ita ta hanyar yi mata fyade, daga nan fa ido ya rena fata, makwabta suka auna ma David na jaki, domin dai David ya daku iya dakuwa da bulala, daga bisani aka barshi ya tafi da kunyarsa.

  Sai dai bayan wannan, David ya fada hannun yansanda sakamakon aikata fashi da makami bayan shi da yan kungiyarsa ta aikata laifi sun yi fashin wani babur a garin Manchie da ke karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna

  DAGA ISYAKU.COM

  Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matashi ya taushe mahaifiyarsa ya yi lalata da ita, ya kuma yi lalata da surukarsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });