Legit Hausa
A bisa dukannanin alamu dai masana harkokin ilimin kimiyyar
rayuwa ta dan adam na daf da kakkabe cutar 'tsufa' daga ban kasa sakamkon wani
binciken da suka gudanar suka kuma samu zarafin gano wani ilimin da da ba'a
sani ba a duniyar kimiyya.
Masanan dai dake a jami'ar Pittsburgh na Amurka sun yi
nasarar gano wani sabon maganin da ake tunanin zai iya sabunta dukannin wasu
kwayoyin halittar bil adama wadanda suka tsufa idan har akayi anfani da shi.
Legit.ng Hausa ta samu cewa sinadarin masanan sun sa masa suna ne da
"Sinadirin Dauwamammiyar Kuruciya".
Da masanan suka yi bayani a mujallar raya fasaha da kimiyya
ta MedicalXpress,tsufa ta samo asali ne daga raguwar wani sinadari mai suna
"Klotho",wanda a yanzu haka suka yi nasarar gano hanyar bunkasa shi.
Sun dai tababatar da cewa,a duk lokacin da aka samu koma baya game da yawan
wannan sinadirin,to za a dinka tsufa babu kakkautawa. Ana kyautata zaton fara
sayar da maganin nan da wani matsakaicin zamani.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI