Legit hausa
An ce wannan shine dalilin da ya sa har yanzu macizai ke da
daraja a garin Machina domin ba a kashe su, kasancewar ana yi ma su kallon
jinin sarauta - Mazauna garin Machina sun yi imanin cewar macijin da aka haifa
tare da sarkin garin ne ya haifi macizan da ake gani na shawagi a fadar sarki
da kewaye Duk da kasancewar jama'a da dama na ganin maciji a matsayin abin
tsoro, sai ga shi a garin Machina da ke jihar Yobe macizai sun zama 'yan gida
don kuwa har gaisuwa su ke kaiwa sarkin garin a fadar sa.
Tarihi ya nuna cewar a wasu shekaru da su ka wuce, matar
sarkin Machina ta haifi'yan tagwaye, mutum da maciji. Kasancewar maciji ba zai
iya zama cikin mutane ba, sai macijin da aka haifa ya sulale ya koma wani
tsauni da ke bayan fadar sarkin Machina.
An ce wannan shine dalilin da ya sa har yanzu macizai ke da
daraja a garin Machina domin ba a kashe su, kasancewar ana yi ma su kallon
jinin sarauta. Mazauna garin Machina sun yi imanin cewar macijin da aka haifa
tare da sarkin garin ne ya haifi macizan da ake gani na shawagi a fadar sarki
da kewaye.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan wannan rahoto, sarkin
garin Machina, Dakta Bashir Albishir Bukar, ya bayyana cewar macijin da ya koma
kan dutse na yin rayuwar sa da iyalinsa, kamar yadda mutane ke rayuwa a gidaje
da iyalinsu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI