Labaran dare daga isyaku.com 13-11-2018

Wani rikici ya kunno kai a makarantar sakandare mai zaman kanta ta Jami'ar Ibadan bayan tasa keyar dalibai zuwa gida.

Iyayen daliban sun yi zargin cewa hukumar gudanarwa makarantar sakandaren ta kulle makarantar tun bayan fara sanya hijabi da dalibai musulmai suka yi.

To amma kuma hukumar gudanarwar makarantar ta musanta batun rufe ta, illa dai ta ce ta haramta a shiga da hijabi a matsayin tufafin makaranta.https://www.bbc.com/hausa/labarai-46198954

An dora alhakin faruwar rikicin kabilanci da haddasa rudani a tsakanin masu zabe da kuma hawa da saukar darajar kudi kan yada labaran kanzon-kurege. 

A yayin da kafar watsa labarai ta BBC ta kaddamar da gagarumin bincike kan labaran bogi a Afirka, mun yi nazari kan labaran kanzon-kurege biyar da suka yi babban tasiri a nahiyar a wata 12 da suka wuce.https://www.bbc.com/hausa/labarai-46179470

Majalisar dokokin Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta dakatar da binciken da take yi wa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne saboda yin biyayya ga umarnin kotu.

A ranar biyar ga watan Nuwamba ne wata babbar kotun jihar ta dakatar da majalisar dokokin daga binciken da take yi wa gwamnan sakamakon karar da wata kungiyar lauyoyi ta shigar inda ta kalubalanci majalisar.

Shugaban kungiyar Barrister Zubairu Muhammad ya yi zargin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.https://www.bbc.com/hausa/labarai-46192459

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta tababtar da cewar ta na kokarin dawo da tsohuwar minister fetur din kasar Diezaini Allison Madueke gida domin fuskantar tuhuma kan batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa da kuma halarta kudaden haramun.http://ha.rfi.fr/afrika/20181111-efcc-za-ta-dawo-da-diezani-najeriya-don-fuskantar-sharia

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce Jam’iyyun siyasa 56 ne cikin 91 da ta yi wa Rijista suka shirya tsayawa takarkaru daban-daban yayin babban zaben kasar da ke karatowa cikin shekara mai kamawa ta 2019.http://ha.rfi.fr/afrika/20181110-jamiyyu-56-ne-cikin-91-za-su-tsaya-zabe-najeriya-inec 

Kotu ta bada damar kama wadanda suka taimakawa Nnamdi Kanu
Buhari na halartar taron zaman lafiya na Paris a FaransaHukumar Kwastam Ta Cafke Mota Shake Da Makamai Da Kwayoyi A Owerri Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya wato, ta yankin “C” dake Owerri na jihar Imo, ta samu nasarar cafke wata...
DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN