• Labaran yau

  Kwarto ya zo bayan maigida ya gayyace shi ya yi zina da matarsa, abin mamaki

  Wani mutum mai suna Macdonald Zuze dan kasar Zimbabwe ya kama kwarto da dabara bayan ya aika wa kwarton wasikar sakon SMS cewa ya zo domin ya yi lalata da matarsa mai suna Esther Mature kuma kwarton ya zo.

  Zuze ya ce ya dade yana zargin cewa matarsa na harka da wani bayan shi, domin baya zama a gida, ko da yaushe yana kan hanyar tafiya daga gari zuwa gari kasancewa shi makaniken manyan motoci ne, kuma ana yawan kiransa domin ya gyara motoci da suka lalace a hanyoyi daba-daban.

  Asiri ya tonu ne bayan Zuze ya bincike wasyar salula na matarsa, sai ya gan wani suna da aka rubuta Mai Takudzwa amma  bayan ya yi bincike kuma sai ya gano hakikanin sunan mai wannan lamba shi ne Kurauwone Kudzaushe kuma kwarton da yake shige yana aikata lalata da Esther a gidan mijinta idan baya nan.

  Daga bisani sai Zuze ya yi wata dabara, ya dinga aika ma kwarton sakon SMS , daga bayanai da kwarto ya rubuto sai Zuze mai gidan Esther ya gano ashe kwarto ya sha aikata zina tare da matarsa Esther, daga bisani sai Zuze mijin Esther ya aika ma kwarton cewa ai Zuze ya sake yin tafiya, saboda haka kwarton ya zo domin su yi lalata.

  Duk wadannan sakonni shi maigidan Esther ne watau Zuze yake aikama kwarto da wayar matarshi Esther ba tare da saninta ba, bayan wani lokaci sai ga kwarton ya zo ya shiga gidan Zuze babu sallama kuma ya nufi dakin kwanciya inda suka saba aikata lalata tare da Esther.

  Shigarsa ke da wuya sai ya rungume Esther nan take shi kuma Zuze mijin Esther ya kuwata jama'a suka zo domin dama ya shaida ma wasu abokansa irin tarko da ya dana ma kwarto kuma kwarto ya fada tarko ya kamashi, domin dai jama'a sun taru domin su shaida irin wannan cin amanar aure da Esther tare da kwarto mai karfin hali suke aikatawa.


  DAGA ISYAKU.COM

  Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwarto ya zo bayan maigida ya gayyace shi ya yi zina da matarsa, abin mamaki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });