Daga Abba M. Zuru
An yi kira ga al’ummar Fulani na kasar Zuru da su kasance masu bin
doka da oda, shugaban Fulani na kasar Zuru kuma shugaban kungiyar
Miyetti Allah na kasa Alhaji Kirwa, ya yi wannan kira a cikin jawabinsa a
wajen taron na al’umman Fulani na kasar Zuru da aka gudanar a babban
dakin taro na Komo Unity Hall a garin Zuru.
Alhaji Kirwa ya kara da cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin
shugaba Muhammadu Buhari da ta jihar Kebbi karkashin gwamna Abubakar
Atiku Bagudu, suna matukar kokarin ganin sun inganta rayuwar Fulani ta
hanyar mayar masu da mashekarinsu,burtallai da gina masu Dam tare da
basu abincin dabbobi.Sakamokon haka godiyansu ga wannan gwamnati shine
tsare doka.
Ardon Zuru ya yi kira ga al’ummar Fulani su guji shaye shaye wanda
shi ne ummul haba’is na samun masu aikata mugan laifuka a cikinsu kamar
fashi da makami da kuma satar mutane.
A nashi jawabi, Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alh.Samaila Yombe
Dabai wanda Alh. Muhammed Kabiru Dabai (Yakaji) ya wakilta, ya bukaci
jama’a su kaurace wa miyagun dabi’u kamar fashi da makami da kuma satar
mutane, ya kuma ankarar da su muhimmancin zaben jam’iyar APC a zabe mai
zuwa.
Daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron akwai ACP Hayatu
Usman wakilin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi, Capt T.W Bawan wakilin
C.O na Barikin Dakkarawa da ke Zuru, da wakilin Maimartaba Sarkin Zuru,
hakazalika shugabannin al’umman Fulani na kananan hukumomin Danko
Wasagu, Fakai da kuma Sakaba duk sun yi jawabi ne kan muhimmancin tsaro
.
Kafin a rufe taron, an raba goro bisa al’adar Fulani na rantsuwa irin ta Filato cewa za a kaurace wa ayyukan ashsha
DAGA ISYAKU.COM
Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI