Type Here to Get Search Results !

Main event

Kebbi: Yansanda sun kama Babangida Garba Gwandu, gwamnati ta yi kararsa

isyaku.com 7-11-2018

Hukumar 'yansandan jihar Kebbi ta kama shugaban Pressure Group na tsofaffin ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi watau Babangida Garba Gwandu ranar Litinin da safe a filin Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a garin Birnin kebbi, kuma yanzu haka tana gudanar da bincike kan zargi da ake yi wa Babangida wanda ya samo asali sakamokon aikata ba daidai ba da kimanin N21m a zamanin shugabancinsa a hukumar KUDA a jihar Kebbi.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Kebbi DSP Danjuma Poppi, ya shaida mana cewa lallai Babangida Garba Gwandu na hannun yansanda a jihar Kebbi kuma suna gudanar da bincike " Babangida yana hannunmu kuma muna gudanar da bincicke ne a kansa, sakamakon kara da Gwamnatin jihar Kebbi ta shigar a kansa saboda aikata ba daidai ba da kudade a lokacin da yake shugabantar hukumar KUDA ".

Babangida Garba Gwandu wanda shi ne Danburam Gwandu, ya shugabanci hukumar Kebbi Urban Development Authority KUDA har tsawon shekara takwas, wanda ake zargin cewa a lokacin ne wasu kudade kimanin Naira Miliyan ashirin da daya N21m aka rasa yadda aka tafiyar da su.

Amma wata majiya da bata son a ambaci sunanta , ta shaida mana cewa " wannan lamarin ya dauki wani salo na rashin adalci, Babangida yana da'awa ne kan a biya su hakkinsu kuma ai ya yi ritaya ne shekara uku da suka gabata , amma sai yanzu aka san cewa babu wasu kudade a lokacin shubancinsa a KUDA? "

A yau Laraba ce kwana ta uku da ake ci gaba da tsarewa tare da bincike a kan Babangida a hannun hukumar yansandan jihar Kebbi. Yunkuri da muka yi domin tuntuban shugabanni da manbobin kungiyar tsofaffin ma'aikata na jihar Kebbi ya ci tura kafin rubuta wannan rahotun.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us. 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies