Legit hausa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent
National Electoral Commission (INEC) ta soma sakin sunayen wadanda za suyi
takarar kujerun gwamnoni a jahohin Najeriya ashirin da hudu da za'a gudanar da
zabukan shekarar 2019.
Haka zalika mun samu cewa hukumar zaben har ila yau ta soma
fitar da sunayen wadanda za suyi takarar kujerun 'yan majalisun jahohin
tarayyar Najeriya dukkan su da za'a gudanar da zabukan su a shekarar ta 2019 Da
dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a
zaben 2019 Legit.ng Hausa ta samu cewa kafin hukumar ta wallafa sunayen, ana ta
samun rikice-rikice a jahohi da dama musamman game da 'yan takarkarin gwamnoni
na jam'iyyar APC mai mulki wanda har ma ake tunanin rikicin ka iya kara
rincabewa.
A wani labarin kuma, Ministan yada abarai na gwamnatin
shugaba Muhammadu Buhari Alhaji Lai Mohammed a ranar Laraba ya ce rahoton da
kwamitin duba zuwa ga yiwuwar karin alabashin ma'aikata da suka mika wa shugaba
Buhari na Naira dubu 30, shawara ce kawai ba wani abu ba.
Ministan yace har yanzu shugaban kasar bai yanke hukunci ba
game da matsayar sa akan batun har sai ya yi duba na tsanaki ga rahoton tukuna
sannan ya fitar da matsayar sa wadda ake sa ran ta zama ta karshe akan batun.
DAGA ISYAKU.COM
Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.