• Labaran yau


  DSS ta kama wadanda suka kashe basarake kayan sun karbi kudin fansa N10m a Kaduna

  Rundunar tsaro ta DSS ta cafke wasu mutane da ake zargin su ne suka kashe wani basarake na Masarautar Adara a jihar Kaduna Dr. Maiwada Galadima dan shekara 64. Wasu gungun batagari ne suka tare ayarin motocin basaraken kuma suka sace shi tare da matarsa a kan hanyar Kachia zuwa Kaduna yan makonni da suka gabata.

  Majiyarmu ta ce bayan bata garin sun karbi kudin fansa N10m, amma sai suka shiga wani kusurgumin daji tare da basaraken kuma suka buda masa wuta da bindigogi ya mutu nan take.Hakazalika wani mutun cikin mutum 8 da batagarin suka yi garkuwa da su da ya yi kokarin tserewa sun harbe shi a kafa a kauyen Katari.

  Karar harbin bindigogi ne ya ankarar da wasu kauyawa a kauyen na Katari, sakamakon haka suka je domin su duba ko miye ya faru, bayan batagarin sun tsere ta cikin kusurgumin dajin.


  DAGA ISYAKU.COM

  Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: DSS ta kama wadanda suka kashe basarake kayan sun karbi kudin fansa N10m a Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama