Legit Hausa
Fadar shugaban kasa tayi alkawarin yin duk abinda ya dace
don ganin babban bankin Najeriya ta dawo da dala biliyan 7 da ta bawa bankuna
masu zaman kansu a 2006. Su dai bankunan sunce kyauta ce gwamnati tayi musu da
kudin jama'a, lamari da shugaba Buhari yace sam-sam ba zai iyu ba, qara wa mai
karfi karfi.
Dole a dawo da kudin Dala biliyan shidda domin talakawa su
mora. Shugaban kwamitin Fadar shugaban kasa akan dawo da kudin kasa, Mista Okoi
Obla-Obono, ya tabbatar da hakan a wani taro da kungiyar ma'aikatan gwamnati ta
shirya akan cece kucen OPL 245 a Abuja. Obla-Obono yace Gwamnatin tarayya tana
binciken wani dan siyasa akan kamfanonin shi 20 a turai don gujewa biyan haraji
ga Najeriya.
Shugaban Kwamitin, ya kuma bayyana wata masana'antar mai da
ta rike dala biliyan 1.9 na kudin shigar Najeriya don haka za'a hukunta
masana'antar da laifin yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI