• Labaran yau

  Dan sanda ya kashe matarsa da danuwanta a cikin Kotu, ya juya ya harbi kansa

  Wani dansanda da ya matukar fusata a lokacin da ake wata shari'a na bukatar da matarsa ta yi na neman Kotu ta kawo karshen aurenta da maigidanta watau dansanda, ya zaro bindiga kirar Pistol ya harbi matarsa da danuwanta a cikin dakin Kotu kai tsaye, lamari da ya sa matarsa da danuwanta suka mutu nan take sakamakon harbi da ya yi masu a a kai daga bisani ya juya bindigar ya harbi kansa, amma bai mutu ba.

  Wannan lamarin ya faru a birnin Durban a kasar Afrika ta kudu ranar Litinin 26-11-2018 da misalin karfe 11:00 na safe.

  Kakakin hukumar yansanda Colonel Thembeka Mbele, ya ce "wanda ya yi kisan jami'in dansanda ne dan shekara 32, kuma ya yi harbin ne yayin da Alkalin Kotun ya je gajeren hutun rabin awa domin shan shayi, daidai wannan lokacin ne wannan dansanda ya harbe matarsa a kai wacce ta shigar da kara domin neman Kotu ta raba aurensu. Hakazalika wannan dansandan ya harbe danuwan matarsa a kai shima, wanda ya rako yaruwarsa watau matar dansanda.

  Yanzu haka dansandan yana cikin yanayi na tsaka mai wuya a wani Asibiti bayan ya juya bindiga ya harbi kansa, amma bai mutu ba".

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin Gyara Wayarka Ka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan sanda ya kashe matarsa da danuwanta a cikin Kotu, ya juya ya harbi kansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });