• Labaran yau


  Dan majalisar APC ya sha dan karen duka, 'yansanda sun yi awon gaba da shi

  Wani dan majalisar dokoki na jihar Akwa Ibom ya sha dan karen duka da safiyar yau, bayan ya shigo harabar majalisar dokoki na Akwa Ibom tare da wasu yan daban siyasa domin su dakatar da zaman majalisa ta hanyar aikata tarzoma.

  Hon. Idongesit Ituen shi ne mai wakiltar mazabar Itu a majalisar dokoki na jihar Akwa Ibom wanda ya canja sheka daga jam'iyar PDP zuwa APC, sakamakon da ya haifar da rigima bayan rahotanni sun yi zargin cewa Kakakin Majalisar dokoki na jihar yana shirin aikata ba daidai ba ranar Litinin dangane da lamarin Hon. Idongesit Ituen.

  Majiyarmu ta ce tuni yansanda suka yi awon gaba da Hon. Idongesit Ituen tare da yan daban siyasa da ya shigo tare da su a harabar Majalisar jihar Akwa Ibom.

  DAGA ISYAKU.COM

  Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan majalisar APC ya sha dan karen duka, 'yansanda sun yi awon gaba da shi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama