Bayan kama Babangida, tsoffin ma'aikata sun karanta Hazbinallahu dubu 70 tare da addu'a

isyaku.com 8-11-2018

Wasu tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jihar Kebbi sun gudanar da addu'a domin neman Allah ya sa gwamnatin jihar Kebbi ta biya su sauran hakkokinsu a filin babban Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a garin Birnin kebbi, a karon farko bayan yansanda sun kama Babangida Garba Gwandu bisa kararsa da gwamnati ta yi a wajen yansanda.

An gudanar da zaman addu'ar da fara karanta Al'quran daga bisani kuma wani Dattijo ya bukaci jama'a su karanta adadin "Hazbinallahu wa ni'imal wakil" sau dubu saba'in wanda aka aiwatar a lokacin wannan zaman da suke gudanarwa kowane ranar Laraba.Hakazalika an bukaci su ci gaba da karantawa a gidaje ko a Masallatan unguwa inda suke zaune.

Sai dai zaman addu'ar na yau bai sami halarcin jama'a da yawa ba kamar yadda aka saba gani a baya, sakamakon haka, wasu tsofaffin ma'aikatan suka koka a jawabi da suka yi wa junansu wani Dattijo ya zargi 'yan asalin garin Birnin kebbi da wasu mazauna cikinta da rashin fitowa a wannan zama, wanda ya ce yawancin tsofaffin ma'aikatan da suka zo wannan zaman addu'a sun fito ne daga Kauyuka da wasu garuruwa da kananan hukumomi da ke kusa da garin Birnin kebbi.

Amma wani Dattijo ya mike tsaye ya shawarci yan'uwansa tsofaffin ma'aikata cewa su cire ganin laifin juna ta hanyar ambaton gari ko ambaton sunan wasu mutane a zancen rashin halaratar zaman addu'ar, kuma sauran jama'a suka aminta.

Bincike da muka yi ya nuna yiwuwa ana kyautata zaton gwamnati zata yi wani abu dangane da lamarin tsofaffin ma'aikatan, hakazalika, mun jiyo cewa akwai yiwuwar wasu wakilai daga yayan kungiyar sun yi ma Abuja tsinke domin fuskantar magabata da wannan matsala tasu.

Saidai yukurin da muka yi domin jin ta bakin Sakataren gwamnati kan lamarin ya gagara, domin mun buga lambarsa ta salula amma bai daga ba kawo yanzu.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without express written permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN