Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya yiwa dukkan ma'aikatan da ke karkashinsa karin albashi zuwa N33,000.
Mohammed El-Yakub, Direktan Gotel Communications, kamfanin
sadarwa mallakar Atiku da ke Yola ya tabbatarwa Sahara Reporters a yau Alhamis
inda ya ce, "za a fara biyan sabuwar albashin mafi karanci na N33,000 daga
watan Nuwamban 2018 kuma karin albashin ya shafi dukkan wadanda ke aiki
karkashin Atiku har da masu hidima a gidajensa."
El-Yakub ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin mutane
100,000 da ke karbar albashi a kowanne wata a karkashin tsohon mataimakin
shugaban kasar.Atiku ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya amince da
N30,000 a matsayin albashi mafi karanci kamar yadda kwamitin albashi da
shugaban kasar ya kafa suka shawarci shi a cikin rahoton da suka gabatar masa.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI