Legit hausa
Titi Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa a karkashin
jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta ce mijinta ba barawo ba ne kuma ba zai taba
satar dukiyar Najeriya ba. Titi ta bayyana haka ne yayin da wata kungiyar mata
ta kai ma ta ziyara a gidanta da ke Abuja.
Ta bayyana cewar Atiku attajiri ne da ba zai taba shiga
takarar neman shugabancin Najeriya don kawai ya yi sata ba. "Ya shiga
takara ne kawai don bawa Najeriya gudunmawa kamar yadda shi ma kasar ta bashi
gudunmawa wajen zama abinda ya zama.
"Atiku ya rasa
mahaifinsa tun yana karami, ya tashi ne a hannun mahaifiyar sa, wacce ya fara
yiwa talla domin samun kudin daukan nauyin karatun sa. Saboda irin kalubalen da
ya fiskanta na tashi a hannun mace, Atiku ya kasance mai matukar tausayi da jin
kai ga mata da matasa.
"Hakan ne ma ya sa shi daukan alkawarin cewar zai bawa
mata da matasa kashi 40% na makaman gwamnati, idan aka zabe shi a matsayin
shugaban kasa," a cewar Titi. Titi ta kara da cewar ana bata sunan Atiku
ne kawai ta hanyar cewa ya yi sata saboda wasu mutane ba sa son ya zama
shugaban kasa.
Ta kara da cewa har yanzu babu wata hukumar yaki da cin
hanci da ta taba gayyatar Atiku domin bincikensa a kan cin hanci. A nata
bangaren, shugabar kungiyar matan, Princess Ngozi, ta ce sun roki Allah domin
ya bawa Atiku nasara a zabe mai zuwa domin ceto Najeriya daga mawuyacin halin
da tsinci kanta.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI