Type Here to Get Search Results !

Main event

An yi wa jirgin Atiku Abubakar binciken kwa-kwaf bayan dawowa daga


Legit hausa

Labarin da muka samu daga majiyar mu ta Blue Print, ya na nuni ne da cewa jim kadan bayan saukar jirgin dake dauke da dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, jami'an tsaro suka shiga bincikar sa.

Tsohon kakakin jam'iyyar na APC, Mista Timi Frank wanda kuma ke cikin tawagar tsohon shugaban kasar shine ya bayyanawa majiyar ta mu hakan a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai Mista Frank ya kara da cewa bayan dukkan binciken su, jami'an tsaron basu samu komai ba a tare da su ko cikin jirgin na su. Mai karatu dai zai iya tuna cewa jam'iyyar APC ta bukaci a binciki dan takarar shugaban kasar idan ya dawo Najeriya.

A wani labarin kuma, Da dumin sa yanzu labarin da ke iske mu na nuni ne da cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya dawo gida Najeriya daga kasar Dubai. Atiku Abubakar din dai ya tafi kasar Dubai ne tare da tawagar sa kunshe da jama'a da dama magoya bayan sa da jam'iyyar Peoples Democratic Party, inda suka shafe kwanaki suna shirya yadda za su tunkari zaben 2019.
 


DAGA ISYAKU.COM


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies