Ababe da ke haddasa mutuwar na miji kan mace yayin jima'i da yadda za a kiyaye

Isyaku Garba 13-11-2018

Sau da yawa akan sami labarin cewa wani mutum ya mutu yayin da yake jima'i da mace, ko matarsa, ko budurwarsa wasu ma sukan mutu ne a kan Karuwai mata masu zaman kansu. Amma miye ke haddasa wannan mace mace a kan mata yayin jima'i ?.

Ko a kwanannan wani mutum ya mutu a kan wata Karuwa a kasar Afrika ta kudu yayin da yake jima' da ita a cikin dakin wani Otel, hakazalika wani tsoho dan shekara 65 ya mutu a kan wata masoyiyarsa yar shekara 35 yayin da yake kanta yana jima'i a kudancin Najeriya mako da ya gabata.

Amma sakamakon wani bincike da muka gudanar a ISYAKU.COM,mun gano cewa mutuwa a kan mace yayin jima'i yana aukuwa ne sakamakon wasu matsaloli da ya hada da:

1. Ciwon zuciya da ba'a kula ba tun farko

Yawancin lokaci wasu mutane kan gamu da ajalinsu a kan mace yayin jima'i sakamakon ciwon zuciya da ke tasowa farat daya a yayin jima'i. Wasu mutane kan yi fama da ciwon zuciya ba tare da sanin cewa suna fama da shi ba, sakamakon haka idan suka fara jima'i kuma zuciya ta fara aiki sosai, domin zuciya ta kan harba da wuri bisa yadda ta saba harbawa, sai mutum ya shake domin zuciyar za ta daina aiki wanda hakaan yana nufin mutuwa saboda nunfashi zai tsaya sakamakon kurewar bugawar zuciya.


2. Hawan jini da ba'a mayar da hankali a kansa ba

Wasu kuma sukan mutu ne yayin da suke kan mace suna jima'i kuma jininsu ya hau matuka amma basu kula ba, sakamakon haka yayin aikata jima'i aikin zuciya a jikin bil'adam aikinsa yana karuwa ne, sakamakon haka jini zai iya hawa har ya wuce kima kuma daga bisani ya haifar wa mutum matsala da ke iya zama mutuwa yayin jima'i. Shi ya sa yake da kyau mai lalurar hawan jini ya dinga kulawa da matsayin jininsa kafin ya yi jima'i da mace.
 

3. Rashin motsa jiki kamar yadda ya kamata

Rashin motsa jiki ma wani hujja ne da zai iya haifar wa mutum matsala da ke iya zama mutuwa a lokacin jima'i, domin idan dama can mutum baya motsa jiki kamar yadda ya kamata, kuma ya kasance a lokacin da yake jima'i ya kwanta a kan mace ta yanayi da zai wahala, nan take zai iya fuskantar matsanancin gajiya da ke iya haifar masa da tseren zuciya , watau zuciya ta fara bugawa da sauri har gudun bugun zuciyar ya wuce lissafin ka'idarta da zata iya dauka, sakamakon haka sai nunfashi ya gagara daga bisani mutum ya ga duhu wanda karshensa shine mutuwa.


5. Yin keta ta hanyar zakewa wajen yin jima'i da karfi yayin kai kawo a kan mace kafin inzali

Wani kuskure da wasu maza ke yishi ne na nuna cewa za su wahalar da mace lokacin jima'i, kuma sakamakon binciken mu ya nuna cewa wadanda suka fi aikata irin wannan hali su ne wadanda suke jima'i da mata masu zaman kansu ko Karuwai. Domin wasu sukan ce sai sun zura wa mace al'aurarsu gaba daya, kuma sukan yi sukuwa ta hanyar kai kawo a kan mace da karfi, ko kuma su bankare mace domin neman biyan bukata. Wani lakaci haka yana haifar wa namiji matsanancin gajiya da tseren bugun zuciya da zai iya zarce lissafi , kuma karshen lamarin shine gazawar numfashi da ke iya sa zuciya ta daina bugawa sakamakon rashin iskan Oxygen.

6. Shaye-shayen magungunan kara karfin mazakuta musamman na Turawa

Sakamakon binciken mu ya tabbatar cewa wasu magungunan sa karfin mazakuta ko na Turawa ko gargajiya su kan haifar da matsala ga wasu maza, wanda ya hada da haddasa bugun zuciya. Wannan yana afaruwa ne sakamakon sinadarin da aka yi amfani da shi wajen hada magungunan.

Abin da ya kamata a kula kafin a yi jima'i

I. A tabbata cewa ba'a yi amfani da wani turare ba bayan an rufe kofar daki kafin a fara jima'i, ko turaren ruwa, ko na fesawa ko turaren wuta. Ammafani da wadannan zai iya tayar da matsalar rashin lafiya ga wasu maza ko mata kafin jima'i, misali kamar masu cutar Asthma- Asthmatic attack, Ulcer-Hyperacidity da Allergy.

2. Samar da wadataccen iska, domin lokacin jima'i miji da mace na bukatar isashshen isakar shakawa mai tsabta.

3. A guji saka ki daidai wajen Socket na wutar lantarki musamman idan akwai wuta ko da ba'a kunnaa Socket din ba. A ja gadon ya dan nisanci wannan Socket na wutar lantarkiko da mita 2 ne.

4. A guji yin jima'i kusa da wayar salula yayin da aka jonata da Charger kuma tana chaji.

5. A guji ajiye waayar salula a kusa da kai, ko a gefen pilo ko a karkashin pilo da za a sa kai a yayin da za a yi jima'i.

6. Idan ka ji zuciyarka ta fara bugawa da wuri fiye da yadda ya kamata, ka dan dakata da sukuwar jima'i da kake yi, bayan komi ya koma daidai sai ka lallaba a hankali ka karasa jima'i da matarka har ka yi inzali.
 
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Domin Flashin ko gyaran wayarka Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN