'Yan sandan jihar Kebbi sun kama masu sace mutane 7 da yan fashi da makami

Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta cafke mutum bakwai da ake zargi da sace mutane domin neman kudin fansa a fadin jihar, sakamakon ingantattun matakai da salo da rundunar ta bullo da su domin ganin an hana masu aikata irin wadannan laifuka sakat a jihar Kebbi. Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya shaida wa manema labarai haka a garin Birnin kebbi ranar Alhamis.

Kwamishinan ya ce an kama wadannan mutane da bindigogi da adduna ranar 2 ga watan Oktoba bayan sun sace  wasu mutane, amma 'yansanda sun ceto mutanen da aka sace kuma tuni suka koma gida.

Hakazalika Kwamishinan ya ci gaba da  cewa, rundunarsa har ila yau ta kama wasu yan fashi da makami bayan sun yi ma wasu mutum biyu fashi, Umar Muhammed da Usman Umar daga garin Bahagu na karamar hukumar Bagudo.

Ya ce an kai ma wadannan mutane farmaki kuma aka karbe kudadensu ta hanyar fashi aka kuma kwace masu babur na kimanin darajar kudi N120.000 ranar 3 ga wataan Oktoba. Ya ce ana kan gudanar da bincike a kan lamarin.

A ci gaba da ayyukanta, rundunar, ta kuma kama wasu fitattun barayi da suka shahara wajen satar wayoyin salula a fadin jihar Kebbi. Wannan ya faru ne sakamakon sata da suka yi bayan sun balle wani shago a garin Argungu suka saci waayoyin salula guda 58. Ya ce an kama su tare da wadanda suke hada baki domin a gudanar da satar wayoyin salula.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN