Type Here to Get Search Results !

Ya karantar da Gwamna Bagudu a 1973/74, yana cikin tsoffin ma'aikata da ke roko a biyasu

Isyaku.com 2-10-2018.

Malam Aminu Usman Kalgo, wani Dattijo ne da wakilinmu ya yi kitibis da shi a wajen taron addu'a da tsofaffin ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi suka gudanar a Masallacin Idi da ke unguwar Gesse a Birnin kebbi ranar Litinin 1/10/2018.Wakilinmu ya gano cewa wannan Dattijo yana daya daga cikin Malaman Pramare da suka karantar da Gwamnan jihar Kebbi na yanzu Sanata Abubakar Atiku Bagudu a shekarun 1973/74 a Makarantar  Pramare ta Karaye da ke karamar hukumar Maiyama a yanzu. Wani abin tausayi shi ne yadda wannan Dattijo ke rokon Gwamna Atiku Bagudu ya yi wa Allah ya biyasu hakkokinsu gaba daya domin su sami  saukin rayuwa a cikin shekaru da suka rage a rayuwarsu bayan sun bauta ma Gwamanatin jiharsu har tsawo dimbin shekaru.

Malam Aminu usman Kalgo, ya bar sashen koyarwa, kuma ya koma Makaranta, daga bisani ya koma bangaren ajiya, kuma ya fara aikin ajiyar kayakin Gwamnati watau Store Officer, har Allah ya yi masa daukaka a bisa tsarin wannan sashe zuwa babban mai ajiye kayan Gwamnati watau Chief Store Officer kafin ya yi ritaya.

Ya yi ritaya a shekarar 2012, ya bukaci a gyara masu Pansho da suke karba kasancewa ana biyan su ne da tsohon tsari biyan Pansho. Ya kuma bukaci Gwamna cewa "Yadda Allah ya taimakeka, ka taimaka ka biya mu kudadenmu na Gratuity da sauran hakkokin mu tun muna da ranmu".

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50,hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gida sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN