Type Here to Get Search Results !

Wasu yan fashi sun atsere daga caji ofis kuma suka sace kayakin ajiya kafin su gudu


Wasu yan fashi da aka kama kuma aka tsare su a chaji ofis na yansanda dake unguwar Ashamu, a rukunin gidaje na Ejigbo da ke birnin Lagos, sun sake tserewa daga chaji ofis kuma suka sace kayakin da aka kama su da shi wanda ke ajiye a matsayin shaida da za'a gabatar a gaban Kuliya.
  
Majiyarmu ta ce yan fashin sun tsere ne daga chaji ofis din da misalin karfe 10 na dare, kuma yayin da 'yansanda ke gudanar da aikinsu.

Hakazalika majiyar mu ta labarta cewa yansanda sun raina yan fashin ne ba tare da sanin cewa wadannan matasan rikakkun takadarai bane da basu da tsoro.

Bayanai sun ce bayan yan fashin sun fasa dakin da aka kulle su suka fita, sai suka balle wata mota kirar Toyota Camry da aka ajiye a chaji ofis mai lamba  LSR 412 AC, mallakin wata mata mai suna Aderieje Rita, kuma suka sace na'ura da ake kira Brain Box mai darajar dubban Naira.
  
Amma daga bisani yansanda sun cafke daya daga cikin yan fashin mai suna Dikachi Onyeze, kuma ba tare da bata lokaci ba suka gurfanar da shi gaban Alkalin Kotun Majistare Mr. T.O. Shomade.

Alkalin Kotun ya bayar da belin  Dikachi Onyeze a kan Naira 100.000. Amma an adana wanda ake tuhumar a Kurkuku kafin ya cika ka'idodin beli, domin za a ci gaba da shari'ar  ranar 29 ga watan Oktoba 2018.  


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN