• Labaran yau

  Tsananin bashi da kwankwadar barasa ya sa mijina ya sheka barzahu

  Wani mutum mai suna  Mphangeli Muncu dan shekara 45daga garin Bergman da ke Mangaung na kasar Afrika ta kudu ya kashe kansa ta hanyar rataya sakamakon tsananin bashi da ake binshi. Tsohon dan barasa, ya kwankwadi barasa ya yi tatil, kana daga bisani ya rataye kanshi cikin dare, sakamakon haka ya mutu ya bar matarsa Miselwa Muncu yar shekara 40 da yara hudu.

  Majiyarmu ta labarta mana cewa Mphangeli ya rataye kanshi ne da wayar lantarki a cikin dakinsa. Matarsa ta ce mijinta dan barasa ne sosai, kuma duk kudin da yake samu yana karewa ne a gidajen giya wajen sayen barasa.

  Miselwa ta ce, ga shi yanzu ya kashe kanshi, kuma ya kara mini tsananin kuncin rayuwa domin ni ce zan biya bashin da ya bari kuma ga yara hudu,. Ta kara da cewa Allah kadai ne zai iya taimaka mata domin ta kula da wadannan yara nata.

  Kakakin yansanda  Constable Peter Kareli ya ce 'yansanda sun fara bincike a kan lamarin.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsananin bashi da kwankwadar barasa ya sa mijina ya sheka barzahu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });