Tabbatar wa Salisu Jarman Koko da kujerarsa daga Abuja, Arc.Sani Bala ya musanta, ina mafita?

Bayan kammala zaben fitar da gwani na 'yan takarar kujerar 'yan majalisar wakilai na tarayya da aka gudanar a jihar Kebbi, wanda ya gamu da tofin Allah tsine dangane da yadda wasu ke zargin an aikata ba daidai ba ta hanyar kwace kujerun wasu 'yan majalisar wakilai da ke kan kujerar a yanzu wadanda suka hada da kujerar Hon Hussaini Kangiwa, Hon Ibrahim Muslim da kuma ta Hon Salisu Garba Jarman Koko. Amma fa sai ga wata sabuwa ta bullo.Domin dai labari ya yi karfi cewa shi fa Hon. Salisu Jarman Koko, ya karbi fom dinsa daga hukumar zabe ta kasa watau INEC wanda ke tabbatar masa da alkawari da uwar jam'iyya APC ta yi cewa a bar 'yan majalisar wakilai da ke kan kujerar su a halin yanzu.

Wani abin dogaro a wannan bayani shi ne yadda muka sami photo copy na wannan fom da Jarman Koko ya cika kuma majiyarmu ta ce har ya kai hukumar INEC. Hakazalika magoya bayan Jarman Koko sun malala a garuruwan Maiyama, Koko da kuma Besse inda suka yi ta murnar samun labarin cewa hedikwatar APC a Abuja ta mayar da hannun agogo baya ga tsarin da aka yi a jihar Kebbi kan sakamakon zaben fitar da gwani na yan majalisar wakilai mai wakiltar Maiyama, Koko da Besse.

Wanda sakamakon haka ne ya sa wani mutum mai suna Nomou ya yi tattaki da kafa daga garin Besse zuwa garin Koko domin murnar jin cewa Salisu Jarma ne zai sake tsayawa takara a jam'iyyar APC.

Amma a tattaunawarmu da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi Arc Bala Sani Kangiwa, cewa ya yi " ni dai a iyakan sanina sunayen wadanda suka ci zaben fitar da gwani da aka yi su ne sunaye da jami'an kwamiti da suka zo suka zo daga hedikwata suka tura kuma ina nan a hedikwata lokaci da suka gabatar da bayanin rahotunsu dauke da duk sunayen".

"INEC bata san wadanda suka ci wannan zaben fitar da gwani ba sai ranar da aka kai mata wannan fom, INEC tana zuwa ne a gabanta a yi zaben fitar da gwani domin su shaida cewa jam'iyya ta gudanar da zaben fitar da gwani, sakamakon haka INEC tana ba hedikwatar jam'iyyu ne su ba 'yan takara.Idan 'yan takara sun cika wannan fom sai jam'iyya ta kai su INEC. A sani na INEC bata ba daidaikun 'yan takara fom".

"sunaye da kwamitin da aka tura Kebbi suka gudanar da zaben fitar da gwani wadannan sunayen ne suka kai ma hedikwatar jam'iyyar APC sannan hedikwata ni suka ba fom na INEC ni kuma na tabbatar cewa wadanda aka bayar da sunayensu bayan sun ci zaben fitar da gwani su ne na ba fom, kuma da suka cika suka kawo mini sai ni kuma na kai su ga hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa, saboda haka ban sane da wancen zance ko wani canji".

Yanzu haka dai, fuskokin magoya bayan Salisu Garba Koko sun yi haske  sabanin yadda suka turmuke a can baya sakamakon bayanai da suka fito daga mahukunta bayan da aka gudanar da zaben fitar da gwani na kujerar dan majalisa mai wakiltar Maiyama , Koko da kuma Besse.

To amma ina gaskiyar wannan lamarin, ganin cewa bangaren Hon. Salisu Garba Koko sun ce tabbas reshe ya juya da mujiya a Abuja dangane da hukuncin mahukunta a jihar Kebbi kan sakamakon zaben fitar da gwani, amma a gefe daya kuma shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi Arc, Bala Sani Kangiwa ya musanta wannan ikirari.

Koma waye ke da gaskiya dai, rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya domin dai wajibi ne gaskiya ta yi halinta.

Daga Isyaku Garba


Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN